Skip to content
September 21, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

Sojoji sun kashe ƴan Boko Haram 6 a Yobe

October 26, 2023 1 minute read

 

Sojojin bataliya ta 159 da ke a garin Geidam a sashe na biyu na rundunar sojin hadaka ta Operation Hadin Kai, sun yi wa ‘yan ta’adda kwanton bauna, wanda hakan ya ba su nasarar kashe ‘yan ta’adda shida. 

A cikin sanarwar da mataimakin mukaddashin darakatan hulda da jama’a na rundunar, Kaftin Muhammad Shehu ya fitar a ranar Alhamis ta ce, sojojin sun kuma kwato bindigun AK-47 biyu, babura biyu da kuma wayar hannu a lokacin fafatawar.

Sanarwar ta ce, sojojin sun yi nasarar ne a aikin da suka yi a ranar 25 na watan Okutubar 2023 a Kauyen Jororo na karamar hukumar Geidam a jihar Yobe.

Kazalika sanarwar ta kara da cewa, wasu daga cikin ‘yan ta’addar sun tsere yayin fafatarwar dauke da harbin albarusai a jinkinsu.

Bugu da kari, sanarwar ta ce, a wani aikin da sojin suka gudanar a ranar Alhamis a kauyukan Bajingo da Kurnawa a yankin Babbangida a karamar hukumar Tarmuwa a Yobe, sojin bataliya ta 233, sun kashe ‘yan ta’adda hudu sun kwato makamai da babura da sauransu.

Jaridar Leadership
Tags: Boko Haram Yobe

Post navigation

Previous: Najeriya Ta Yi Nasara Kan Rikicinta Da Kamfanin P&ID A Kotun Ingila
Next: Ƴan bindiga na cin karesu ba babbaka a Katsina

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.