Labarai

An cafke wani malamin addini da sassan jikin mutum a  Oyo

Rundunar ƴan-sanda reshen Jihar Oyo ta kama wani malami mai shekaru 45 bisa zargin mallakar sassan jikin mutum danye cikin makon nan.

Jamiin hulda da jamaa na rundunar, Sufurtanda Adewale Osifeso, ne ya bayyana hakan a Shalkwatar rundunar da ke Ibadan yayin da gabatar da wanda ake zargin.

Ya kara da cewa yansanda sun kama mai laifin ne a ranar 6 ga Nuwamba, 2023 da misalin karfe 10:00 na safe a unguwar Ogbere-tioya, Ibadan.

Rundunar yansandan ta ci karo da malamin ne bayan gudanar da bincike a tsanake tare da bin diddigi a kusa da yankin Ogbere-tioya, Ibadan, dake karkashin Karamar Hukumar Ona-ara.

Osifeso ya yi zargin cewa an samu nasarar cafke shi ne biyo bayan rahotannin sirri da aka samu daga jamaa.

 

Osifeso ya ce, An samu wanda ake zargin dauke da wasu kayayyaki da ake zargin sabon kan mutum ne da hannaye biyu, ya ce wani dan Tijjani Waheed ne ya ba shi.

Da yake magana da manema labarai, wanda ake zargin ya amsa cewa sabon kan mutum da hannaye biyu da aka samu a hannunsa na tsafi ne.

Ina da mata daya da yaya biyu kuma ina shan wahala, ba zan iya daukar dawainiyarsu ba.

Na hadu da wani Waheed, wanda shima Malamin Addinin Islama ne a wajen Mauludi, inda muka yi hira a nan ya ke gaya min cewa ya san yadda ake yin kudi amma aikin zai bukaci amfani da sassan jikin mutum.

Na gaya masa cewa ban san a inda zan samu sassan jikin mutum, amma ya ce in jira shi zai neme ni. Daga baya muka hadu da shi ya kawo mini sassan jikin mutum a Amuloko inda muka hadu da safe kuma na ajiye shi a ofishina inda nake sauraron mutane masu neman taimako.

Kawai ban Ankara ba sai na ga yansanda sun zo domin su yi binciki a ofishina a ranar da Waheed ya ba ni sabon kai da hannaye biyu, in ji shi.

Jaridar Leadership