Home Labarai Ayyukan Shugaba Buhari Sun Nuna Inda Basukan Da Yake Ciyowa Ke Tafiya...

Ayyukan Shugaba Buhari Sun Nuna Inda Basukan Da Yake Ciyowa Ke Tafiya — Fashola

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya ce aikace-aikacen raya kasar da Gwamnatin Tarayya take zubawa a fadin kasar sun nuna inda kudin da take ciyo wa bashi suke tafiya.

A cewar Ministan, gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta gaji Naira biliyan 18 kacal a matsayin kudaden ayyuka lokacin da ta karbi mulki a 2015.

Hajarul Aswad: Muhimman abubuwan game da dutse mai daraja
An bankado ma’aikatan bogi 268 a Babbar Kotun Kogi
Fashola dai na jawabi ne yayin bude taron masu ruwa da tsaki kan ayyuka na Najeriya karo na 28 da ya gudana a Kano ranar Alhamis.

Ya ce, “Amma kasafin kudinmu na farko [a 2016], mun ware sama da Naira biliyan 250, kari a kan Naira biliyan 18 din da muka gada a 2015, an sami karin kusan kaso 1,000 ke nan, duk da yake a lokacin farashin danyen mai ya fadi a kasuwar duniya. Ba mu kara haraji ba.

“Saboda haka, dole ta sa muka ciyo bashi. Idan kuka ji ana tambayar inda kudaden [bashin] suka shiga, to suna wajen ayyuka.

“A kodayaushe nakan tambayi mutanen da ke cewa kada a ciyo bashi, ba wai cewa nake kada mu damu da basukan ba, amma waye ba ya son aiki? Wacce jihar ce ba ta son wadannan ayyukan sai mu cire ta, ka ga an sami ragin basukan ke nan,” inji Fashola.

Ministan ya kuma ce ya zuwa yanzu, gwamnatin ta kammala aikin tituna da suka kai kilomita 1,800 a fadin kasar nan, kuma za ta kammala ragowar kafin karewar wa’adin gwamnati mai ci a 2023.

Shi ma da yake nasa jawabin, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce akwai bukatar a sami hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi wajen yin ayyuka, sannan ya yaba wa Buharin kan ayyukan da ya kawo wa jihar Kano.

Aminiya ta rawaito cewa taron na kwana biyar, wanda aka fara shi tun ranar Litinin mai taken: “Zamanin kammala ayyukan da gwamnatoci suka fara”, ya tattaro masu ruwa da tsaki a fannin ayyuka daga dukkan jihohin Najeriya.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.