Latest:
Labarai

Bam Ya hallaka Mutane 20 A Yobe

 

Akalla mutane 20 ne suka mutu bayan da wani babur ya taka wani bam da ‘yan ta’addan Boko Haram suka dasa a jihar Yobe a yammacin ranar Talata.

Bam din ya tashi ne da misalin karfe 6:30 na yamma a kauyen Goni Mittiri da ke garin Gumsa a karamar hukumar Gaidam a jihar, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa LEADERSHIP.

An ruwaito an yi jana’izar kimanin mutane 17 da harin Boko Haram ya rutsa da su a safiyar ranar Litinin, yayin da suke dawowa daga makabarta, yayin da wani abu ya fashe.

Wasu majiyoyi sun ce an birne bam din ne a gefen hanya.

Daya daga cikin mazauna yankin ya ce, “Mun kidaya jimillar mutane 20 a wurin da lamarin ya faru, za mu yi jana’izar mutum 11 a wannan dare (ranar Talata).

“Sauran mutane tara da suka mutu za a birne su a gobe Laraba da karfe 9 na safe amma akwai ma’aurata – mata da miji wanda suke karbar magani a asibiti saboda raunukan da suka samu sakamakon fashewar bam din.”

Jaridar Leadership