Home Labarai Buhari Ya Bukaci Majalisa Ta Kara Yawan Kudaden Tallafin Man Fetur Zuwa...

Buhari Ya Bukaci Majalisa Ta Kara Yawan Kudaden Tallafin Man Fetur Zuwa Tiriliyan 4

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta amince da karin kudirin kudi da aka kiyasta na tallafin man fetur na shekarar 2022, daga naira biliyan 442.72 zuwa naira tiriliyan hudu.

Majalisar dattawan ta kuma samu wata takarda, shugaban Kasa na neman majalisar ta amince yayo rance kuma yayi gyara ga tsarin kasafin kudi na 2022.

Bukatun na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 5 ga Afrilu, 2022, wadda shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta jiya a zaman majalisar.

Shugaba Buhari, a cikin wasikar, ya ce gyara ga tsarin kasafin kudi na 2022 ya zama wajibi bisa la’akari da canje-canje da aka samu a kasuwannin duniya da na cikin gida.

A cewarsa, bukatar ta biyo bayan hauhawar farashin danyen mai a kasuwar mai, wanda hakan ya faru ne sakamakon yakin Rasha da Ukraine da kuma yawaitar masu satar danyen mai.

“Shawarar dakatar da cire tallafin man fetur a daidai lokacin da farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabo ya yi matukar durkusar da kudaden shiga na gwamnati,” in ji shi


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.