Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Zamfara ta tabbatar da sace wasu Éalibai mata huÉu na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tsafe.
Kakakin rundunar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillacin Labarai na Æasa, NAN, a Gusau a yau Laraba.
Shehu ya ce an yi garkuwa da daliban ne a daren ranarTalata.
âWadanda ake zargin âyan bindiga ne sun kai hari a dakin kwanan dalibai da ke wajen makarantar, wani gidan haya a garin Tsafe.
âDa samun rahoton, jamiâan tsaro sun fatattaki masu garkuwa da mutane, daya daga cikin daliban biyar da aka sace ta tsere daga hannun Æ´an bindigar amma kuma sun gudu da sauran hudun,â in ji Shehu.
Kakakin ya Æara da cewa rundunar ta kai jamiâan ta na sashin nema da kubutarwa domin haÉa kai da sojoji don a tserar da Éaliban.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








