Farashin dala na faÉuwa a kasuwannin canjin kuÉaÉe a Najeriya daga naira 940 zuwa naira 890 a safiyar Laraba kamar yadda bayanan da BBC ta samu daga kasuwannin canji a birnin Legas da ke kudancin Æasar suka nuna.
Bayanan sun nuna cewa a safiyar jiya Talata, an sayar da dalar kan naira 940, da yamma kuma, ta fadi zuwa naira 927 a kasuwannin canjin a Legas.
Wannan na zuwa ne bayan ganawa da muÆaddashin gwamnan babban bankin kasar, Folashodun Shonubi, ya yi da shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin a fadarsa da ke Abuja, kan yadda za a farfaÉo da darajar Naira.
A kasuwannin canji na Abuja kuma, a safiyar Laraba, dalar ta fadi zuwa naira 900, inda a safiyar Talata, aka sayar da ita kan naira 947, da dare kuma, ta sauka zuwa 910.
Haka ma Kano da ke arewacin Æasar, bayanai daga kasuwannin canji na nuna cewa dalar ta faÉi daga naira 946 a safiyar jiya Talata zuwa naira 900 a safiyar yau Laraba.
A daren jiya dalar ta fara sauka a kasuwannin canji na Kano inda ta sauka zuwa naira 927.
Wannan lamari na nuna cewa darajar kuÉin naira ta fara farfadowa.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








