Labarai

An hallaka sojojin Nijar 17, an raunata 20

Akalla sojojin Nijar 17 suka rasu sakamakon wani hari wanda ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai shi kan iyakar Mali.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wata sanarwa da ma’aikatar tsaro ta kasar ta fitar inda ta ce an yi kwanton bauna kan dakarun ne a garin Koutougou.

Ma’aikatar tsaron ta bayyana cewa baya ga sojojin da aka kashe, akwai wasu sojoji 20 da suka samu raunuka, shida daga cikinsu sun samu mummunan rauni.

Sama da mahara 100 sojojin suka halaka a samamen da suka kai, in ji sojojin.

Rikicin masu ikirarin jihadi ya jefa yankin Sahel cikin wani hali tsawon shekaru, inda lamarin ya yi kamari a Mali a 2012 kafin ya bazu zuwa Nijar da Burkina Faso a 2015.

TRT Afrika Hausa

Leave a Reply