Skip to content
September 20, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • News

Gidauniyar Wunti Al-khair Ta Yi Gargadi Kan Masu Amfani Da Sunanta Ba Bisa Ka’ida Ba

July 19, 2025 2 minutes read

Daga Mubarak Aliyu Kobi

Gidauniyar Wunti Al-khair Foundation ta nesanta kanta daga kungiyoyi da wasu daidaikun mutane da ke gudanar da ayyuka da sunanta ba tare da izini ba, tana mai bayyana irin wannan aiki a matsayin sojan gona.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Gidauniyar ta jaddada cewa dole ne a guji amfani da sunanta wajen gudanar da shirye-shirye, taruka ko bayar da tallafi, koda kuwa da kyakkyawar manufa, ba tare da samun izinin ta ba. Ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen hana bata-gari amfani da sunan Gidauniyar wajen aikata ayyukan da ba su dace ba.

Gidauniyar ta kuma bayyana cewa ba ta da alaka da harkokin siyasa, tare da jan hankalin jama’a kan cewa ba ta amincewa da duk wani yunkuri na amfani da sunanta wajen shirya taron siyasa ko amfani da kafafen yada labarai wajen yada manufofin siyasa.

Ta kara da cewa kamar yadda aka saba, Gidauniyar Wunti Al-khair Foundation na gudanar da ayyukan jin kai da bayar da tallafi ga mabukata a cikin al’umma, ba tare da wata manufa ta daban ba, tare da kiyaye adalci ba tare da nuna banbancin addini, kabila ko jam’iyya ba.

Gidauniyar ta bayyana cewa wannan gargadi ya zama dole domin jan kunne, tare da sanar da cewa za ta dauki mataki kan duk wanda ya yi kunnen uwar shegu, inda ta ce za ta bai wa hukumomin tsaro damar yin aikinsu idan aka ci gaba da karya wannan umarni.

“Idan kunne yaki ji, jiki ya tsira,” in ji sanarwar.

– Hukumar Gudanarwa, Wunti Al-khair Foundation

Tags: Bauchi state police command Department of State Services Wunti Alkhair Foundation

Post navigation

Previous: NIPR To Hold Five-Day Retreat for Newly Elected Council Members
Next: Over 300 Benefit from Free Screening and Surgery on Cataract Conducted by Wunti Alkhair Foundation in Bauchi

Related Stories

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.