Latest:
Labarai

Gobara ta lakume rayukan Mutane 64 a Afirka ta Kudu

 

Mutum 64 ciki har da kananan yara sun mutu a gobarar da ta tashi a wani bene da ke birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

Hukumomin agaji a kasar sun ce wasu mutum 43 sun samu kuna da wasu raunuka, ciki har da wadanda numfashinsu ya sarke shakamakon shafar hayakin gobarar da ta tashi tun kafin wayewar garin Alhamis.

“Mutum 64 ne aka tabbatar sun rusu, ciki har da kananan yara bakwai,” ciki har da dan kasa da shekaru biyu, in ji kakakin hukumar agajin gaggawa ta kasar Robert Mulaudzi.

Ya bayyana cewa an kai wadanda suka samu ranun asibiti, kuma jami’an kwana-kwana na kokarin shawo kan gobarar.

Kawo yanzu dai ba a sanar da musabbabin gobarar ba.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply