Home Labarai Kenya na fama da karancin kwaroron roba 

Kenya na fama da karancin kwaroron roba 

Kenya na fama da karancin kwaroron roba da take rabawa kyauta ga maza saboda ragin tallafi da take fuskanta daga kungiyoyi. Ƙasar na bukatar akalla kwaroron roba miliyan 400 a kowacce shekara.

Gwamnati a yanzu na iya raba kwaroron roba miliyan 150 ne kacal, wanda bai kai rabin abin da ake bukata ba.

Gidauniyar AIDS Foundation, ta yi gargaÉ—in cewa idan ba a shawo kan matsalar ba, Kenya na iya fuskantar kalubalen yaÉ—uwar cututtuka irinsu HIV, da cutar da ke yaÉ—uwa ta jima’i da É—aukar cikin da ba a so.

Wani babban jami’i a hukumar da ke yaÆ™i da cututtuka masu yaÉ—uwa ya ce akwai bukatar É—aukan matakai a cikin gaggawa.

Ƙwararru a fannin lafiya da ‘yan majalisa da Æ™ungiyoyin tallafi za su gudanar da wani taro nan da kwanaki uku a birnin Mombasa domin shawo kan matsalar da kuma samar da karin magungunan HIV.

BBC Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.