Dan majalisar dokokin jihar Kebbi, dake wakiltar mazabar Argungu, Alhaji Umar Na’amore, yayi kira ga gwamnatin tarayya data jihar Kebbi da su hanzarta yin feshi ga tsuntsayen jan baki da suka fantsama a gonakin manoma a jihar.
Na’amore, yayi wannan kira ne a hirarsa da kamfanin dillancin labaru ta Najeriya NAN a birnin Kebbi.
Yace, daukar matakin gaggawa zai kawo karshen tsuntsayen da yanzu haka ke cigaba da lalata amfanin gona a yankin.
A cewarsa, jan baki sun lalata a kalla kadadar gonakin noma dubu 95 na shinkafar rani inda lamarin ya fi muni a yankin.
Na’amore, yace abu dake adane cewar yawancin manoman sun runtumo basussuka ne daga kamfanoni kamar Labana da WACOT da sauransu, domin yin noman shinkafa da nufin samar da wadataccen abinci ga kasarnan.
Manoma na fiskantar shigowar tsuntsayen ne daga makwabtan kasashen Benin da Nijar.
Dan majalisar ya bidi daukin gaggawa daga gwamnati, tare da neman kamfanonin da su daga kafa wa manoman wajen biyan bashin zuwnan nan da shekara mai zuwa.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.