Majalisar Dokoki ta Kasa ta ce Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da Naira tiriliyan 19.76 a matsayin kasafin shekarar 2023 a watan Oktoba mai kamawa.
Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya ce Buhari zai gabatar da kasafin ne ga Majalisar Dokoki ta Kasa kafin majalisar ta tafi hutu a watan Oktoba.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake duba aikin gyaran Majalisar da ake fatan kammalawa a watan Agusta, 2023.
Kasafin wucin gadi mai gajeren zango da Gwamnatin Tarayya ta gabatar wa Majalisar Dokoki ta Kasa ya nuna gwamnatin na hasashen kashe Naira tiriliyan 19.76 a shekarar 2023.
Gbajabiamila wanda ya yaba da saurin aikin da aka fara a watan Agusta, ya bukaci dan kwangilar ya tabbata an kammala a kan lokaci, tare da cewa Majalisar ba za ta lamunci aiki mara inganci ba.
Ya kuma saurari bayani daga dan kwangilar kan irin gyare-gyaren da za a yi a wuraren zaman shugabanni da sauran mambobi da ma’aikata da sauran wurare a cikin zauren Majalisar da kuma rufinsa.
A cewarsa, gyare-gyaren za su taimaka wa Majalisar wajen gudanar da ayyukanta daidai da takwarorinta a fadin duniya.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.