Melody Agwom Dauda
A matsayina na yar jarida, na samu damar bayar da labarai daban-daban a fadin Najeriya da ma duniya baki daya, amma babu wanda ya bar tabo maras gogewa a gare ni face labaran cin zarafin mata da ƴan mata. Yawan zalunci, nada mummunan tasiri ga iyalai da al’ummomi, rashin mayar da martani da gazawar tsarin da ke ci gaba da kawo wannan annoba sune suka tilasta ni in haskaka wannan batu mai mahimmanci.
Cin zarafin mata da yan mata ya zamto annoba da ya shafi miliyoyin ‘yan Najeriya. A bisa wasu alƙaluma da hukumar kididdigar jama’a ta kasa wato National Demographic and Survey (NDHD) ta fitar a shekarar 2018, daya daga cikin mata uku a Najeriya ta fuskantar cin zarafi, yayin da daya cikin biyar ke fuskantar cin zarafi ya Allah ko ta hanyar fyade. Ƙididdiga na da ban mamaki, amma dukda haka suna ba ɗan wani taƙi ne labarin kawai.
A yayin da na zagaya a sassa daban-daban na al’umma, ta yadda nayi katarin magana da wadanda abin ya shafa a yanzu, kamar masu fafutuka da masu tsara manufofi, na ga mummunan tasirin da cin zarafi yayi ga rayuwar mata da ‘yan mata. Farko na hadu da wata yarinya ƴar kimanin shekara 23, wadda aka yi mata fyade a lokacin tana ƴar shekara 17 kacal, wadda ta ba da labarin yadda wasu gungun mutane hudu suka yi mata dukan tsiya har ta kai ga suma.
Hadiza (an sakaye asalin sunanta) ta bar gidan su inda ta nufi gidan su abokiyar karatun da basuda nisa domin karbo aron littafi karatu wato “handout” domin yin aikin gida da aka basu, wanda zasu kai a makon da zasu koma makaranta, a lokacin bai wuce ƙarfe 7:30pm na dare ba amman mutane kadan ne kai zirga zirga a titinta. Sai wasu yara ƴan unguwa da aka sansu kuma ake makwabtaka da su suka tare ta. A lokacin bata basu hankalin ta ba, hakan yasa suka ji haushi sannan suka ka da ita a ƙasa, ba su barta tayi kuka ba domin a kawo mata agaji domin kuwa ɗaya daga cikin su ya cusa mata riga a bakinta. Suka yayyage rigarta cikin rashin tausayi sannan suka mata abinda suka ga dama, sai suka buge ta a kai tare da barin ta a wajen kamar wadda ta mutu.
Da Hadiza ta dawo hayyacinta, wasu mutanen kirki sun ɗauke ta inda suke wuce da ita gida.Ta ba da labarin irin azabtar wa da aka yi mata ga mahaifiyarta da ƴar uwarta wadanda suka kasance a gida a lokacin da aka kawo ta gida, sai suka yanke shawarar cewa wannan labari ya zama sirri a tsakaninsu, ba wanda zai iya sani, saboda sunan gidan zai iya ɓaci. An kai ta asibiti domin a yi mata maganin raunukan da ake gani sai dai me zai faru? ba komai, eh ba bu komai. Daga baya ta koma makaranta, kuma abinda ba’a sani ba shine, waɗanda suka keta mata haddi suna zuwa wannan makaranta tare da ita, tana ganinsu a koda yaushe, a duk lokacin da ta gansu tana tunowa da abinda ya faru da ita, abu mafi muni ma shine a duk lokacin da suka ganta sai sun bushe da dariya sannan suke nuna ta da yatsa a duk lokacin da suka hadu. Abun kaico, Hadiza ba ta samu adalcin da ya kamata ta samu ba_ godiya ga danginta amma duk da faruwar wannan lamari ban taba ganin irin karfin hali kamar haka ba, wanda aka sanya wa baƙin ciki, akacu amanar sa amman kuma an bar mata azaba ta hankali da ma bacin zuciya, duk da haka ta zaɓi ɗaukar shi da zuciya ɗaya.
Wannan ba yana nufin babu taimako ga wadanda abin ya shafa bane da ke neman adalci kan duk wani cin zarafin da aka yi musa ba. Wannan ya bayyana a cikin lamarin Asma’u (an sakaye sunanta na gaskiya), wacce aka yi mata fyade a cikin wani masallaci da ke unguwar Igbo Quarters da ke cikin karamar hukumar Bauchi a jihar Bauchi. Jamilu Abdullahi, mahaifin Asma’u ya bada labarin abin da ya faru biyo bayan cin zarafin da aka yi wa diyarsa. Da kuma yadda ya yi kokarin komawa wani wuri da ba a bayyana ba don hankali da lafiyar ƴarsa saboda yadda kowa yake nuna ta da yatsa a duk lokacin da ta fita wasa da yara abokanta.
Malam Jamilu Abdullahi ya ci gaba da yin karin haske kan matakin da gwamnatin jihar Bauchi ta dauka na ganin an hukunta wanda ya ci zarafin ƴarsa ta fuskar doka. Uwargidan Gwamnan ta dauki yarinyar da mahaifinta, mahaifiyarta tare da rakiyar manyan jami’an gwamnati zuwa asibiti, inda ta tattara dukkan shaidu da rahotannin bincike, sannan bayan binciken jami’ai sun tabbatar da cewa an yi fyade, sannan kuma an kama wanda ya aikata laifin, an gurfanar da shi a gaban kuliya inda kuma aka yanke masa hukuncin dauri a gaban kotu. Wannan bai tsaya a nan ba, an watsa sakamakon wannan shari’ar a kafafen yada labarai na jihar.
Cin zarafi da ake yi wa mata da ƴan mata koma baya ne ga zaman tare cikin lumana domin yana shafar rayuwar wadanda suka fuskanci cin zarafin, ta hanyar sauya dabi’arsu, yana shafar dangantakarsu da mutane da kuma jefa su cikin yanayi na damuwa ta hanyar kebewa daga mutane da kiyayya a dabi’a, ta yadda hakan ke toshe musu damar samun dammaki a rayuwar su. Wannan tauye hakki ne na kai tsaye. Sauran nau’o’in tashin hankali a tsakanin ma’aurata shima wani cin cin zarafi ne, domin kuwa ya bar miliyoyin mata da ƴan mata da tabo a zukatan su da jikinsu na dindindin.
An gano hanyoyi da dama wajen magance matsalar cin zarafin mata da ƴan mata. An ƙara rarraba waɗannan ƙalubalen zuwa matakai kamar haka:
Ka’idoji masu zurfi na al’adu da na gargajiya. Najeriya kasa ce mai bambancin al’adu da ke da kabilu sama da 250, kowannensu yana da nasa al’adu. Wasu daga cikin wadannan al’adu suna cin zarafin mata da ƴan mata. Mata da ƴan mata na fuskantar kalubalen zamantakewa a cikin al’umma, suna fama da tashin hankali kamar cin zarafi, lalata da yara, muzguna musu, fyade da barinsu cikin shiru.
Har ila yau, Nijeriya al’umma ce inda maza ke da iko da tasiri. Hakan na iya sanya mata da ƴan mata su gaza fitowa domin yin magana kan cin zarafin da aka musu harma da neman adalci. Maza suna ganin haƙƙinsu ne su daki mata koma suyi amfani dasu a matsayin duk abin da suke sha’awa ba tare da an tambaye su ba kamar yadda ake karin magana da cewa “DUNIYA NA NAMIJI NE” inda ake cin zarafin mata da ƴan mata daban-daban kuma ba a ƙalubalantar haka.
Wani kalubale kuma shi ne batun kyama da kunya. Abin kunya ne a yi lalata da ita koda kuwa ta jiki ne, abin mamaki!. Wadanda suka fuskanci cin zarafi musamman mata da ƴan mata sukan fuskanci wulakanci da kunya, wanda hakan kan iya hana su neman taimako ko bayar da rahoton halin da suka samu kansu.
Wani mai sarauta, Hussaini Abubakar othman, Dan jikan Bauchi kuma Hakimin Miri a karamar hukumar Bauchi ya bayyana kalubalen da sarakunan gargajiya ke fuskanta wajen magance matsalar cin zarafin mata da ƴan mata da ake yi, inda yace wasu iyalai sukan boye cin zarafin mata da ƴan mata hanyar kare masu laifi daga fuskantar shari’a saboda dangantaka ta iyali, abota ko kuma a wani lokacin saboda ɗan wani tagomashi.
Kalubalen hukumomi da na tsari sun ba da gudummawa ga yanayin tafiyar hawainiya wajen hukunta mafi yawan masu aikata laifin cin zarafin mata da ƴan mata. Wasu daga cikin hukumomin tabbatar da doka da shari’a a Najeriya suna da rauni, ba su da inganci ko ma sun tsufa, wanda hakan ke sanyawa a gaza hukunta masu laifin cin zarafin mata da ƴan mata wajen ganin an gurfanar dasu domin su girbi abinda suka aikata.
Har ila yau, rashin wadata da kudade ya zamo wani babban kalubale. Habiba Usman Sa’ad, Amira na kungiyar mata musulmi ta Najeriya (FOMWAN) reshen jihar Bauchi, wata kungiya ta addini, ta shaida min yadda magance cin zarafin mata da ƴan mata ke bukatar kudade masu yawa amma galibi ba su da isassun kayan aiki da kuma kudade don magance matsalar, matsalar samar da matsuguni da kuma kula dasu na daga cikin manyan kalubale ta hanyar kulawarsu. Talauci da rashin daidaiton tattalin arziki na a matsayin babban kalubale a Najeriya kuma zai iya ta’azzara cin zarafin mata da ƴan mata.
Yawancin ƴan Najeriya ba su da ilimi dama sanin ya kamata game da cin zarafin mata da ƴan mata wanda zai iya yin wahala a mayar da martani ga lamarin. Iyakantaccen damar samun kiwon lafiya musamman a yankunan karkara na iya sanya wa wadanda suka fuskanci cin zarafi musamman mata da ƴan mata sun gaza samun kulawar da suke bukata. Rikice rikice dama rashin tsaro a cikin ƴan shekarun nan da ake gani a Najeriya, sun jefa mata da ƴan mata cikin hadarin fuskantar kowane nau’i na tashin hankali, kamar karin magana ne dake cewa, “Mata da ƴan mata ganimar yaki ne”.
Wadannan kadan ne daga cikin kalubalen da ake fuskanta na magance matsalar cin zarafin mata da ƴan mata a Najeriya,kuma domin magance wadannan kalubale ana bukatar tsayin daka daga bangarori da dama daga gwamnati, kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da daidaikun mutane.
Duk da tarin kalubalen da ake fuskanta wajen magance matsalolin cin zarafin mata da ƴan mata, na ɗan ga an samu ci gaba. Domin kuwa na gana da masu ruwa da tsaki dake aiki tuƙuru don wayar da kan jama’a da tallafawa waɗanda suka tsira. Na kuma yi magana da masu tsara manufofin da suka himmatu wajen karfafa dokoki da manufofi don kare mata da ‘yan mata. Na ga yadda al’ummomi suka fito suna masu cewa A’a da duk wani nau’i na cin zarafi da kuma na’am da bayarda ƴancin mata.
To, wasu irin ci gaba ne aka samu wajen tunkarar kalubalen cin zarafin mata da ƴan mata a Najeriya?
1.karfafa dokoki da tsare-tsare :Gwamnatin Najeriya ta taka rawar gani wajen karfafa dokoki da manufofin kare mata da ƴan mata. Dokar haramta cin zarafi ga mutane na shekarar 2015, doka ce mai matukar muhimmanci domin kuwa ta haramta duk nau’i na cin zarafi musamman ma a cikin gida, fyade da kuma yiwa mata kaciya.
Bar. Elizabeth George, wata kwararriyar lauya ce, wacce kuma itace babbar darakta a gidauniyar Child is Gold foundation (CIGF), ta kasance mai tabbatar da bin doka da oda tare da gwamnatin jihar dangane da matsalolin cin zarafin mata da ƴan mata tare da yin karin haske kan dokoki da tsare-tsare da ake da su na kare mata da ƴan mata a Nijeriya ciki harda dokar nan ta haramta cin zarafin jinsi wato VAPP Law, wadda a halin yanzu ake amfani dashi a mafi yawan jihohi a fadin tarayyar kasar nan, Jihar Bauchi na daga ciki, sai kuma ƴancin yara da a halin yanzu, gidauniyar Child is Gold Foundation CIGF tare da gidauniyar ASH Foundation a halin yanzu suna aiki tare wajen tabbatar an samar da dokar da ta zama dole, ta kafa wani wajen ajiye audugar mata a makarantun firamare da sakandare a jihar.
Kowace rana, akwai dokoki da yawa waɗanda ke taimakawa da kuma tallafawa mata kan batutuwan jinsi. Dokar nan ta VAPP law ta kunshi batutuwa da dama a tsarin hukunta masu cin zarafin mata da ƴan mata. Sai dai duk da irin gibin da aka samu a cikin wadannan dokokin, dokar ta VAPP ta fito fili domin bayyana takunkumi daban-daban ga wadanda suke yin yunkurin hana yin adalci daga wadanda suka aikata laifin.
Babu wasu kungiyoyin gwamnati da kungiyoyin bayar da agaji harma da shugabannin masu hangen nesa a jihar da suka nuna jajircewa da goyon bayan kokarin gwamnati wajen yaki da wadannan matsaloli na cin zarafin mata da ƴan mata ta hanyar kashe kudadensu da lokacinsu wajen horar da mambobin kungiyarsu ta hanyoyi daban-daban don kai dauki mai kyau ga buƙatun gaggawa na samar da wuri mai aminci ga waɗanda suka tsira daga cin zarafi da kuma tabbatar da an hukunta masu keta musu haddi.
A kokarin da gwamnati ta yi na samar da ayyukan tallafi ga wadanda suka fuskanci cin zarafi, a Bauchi a yanzu, akwai cibiyar SAK CENTER da ta kunshi, wuri g wadanda suka tsira daga cin zarafi za su iya samun damar kai ƙara ga jami’an ‘yan sanda, lauyoyi, sauran ayyukan jin kai da kula da lafiyar kwakwalwarsu ga wadanda suka fuskanci wannan matsala ta cin zarafin jinsi. Hanya ce mai kyau, saboda a shekarun baya ba a samu irin wannan ba. Wani abin sha’awa shi ne, akwai tsarin da gwamnatin jihar ta gindaya saboda abubuwan da gwamnati takeyi ba ta da su a baya na magance cin zarafin mata da ƴan mata, amman a yanzu sun bada dama ga hukumomi da kungiyoyin da ke aiki a kan irin wadannan batutuwa domin su cigaba da kula dasu.
Akwai mutane da yawa da ake yanke musu hukunci a matsayin masu cin zarafin jinsi. Abin da aka samu a shekarun baya kafin kafa dokar nan ta VAPP Law a shekara ta 2015 shi ne duk wanda aka samu da laifin cin zarafi jinsi, zai fuskanci hukunci ba tare da la’akari da shi waye ba, ko da kuwa za su iya yin hakan kuma su sami kubuta.
An samu raguwar yawaitar cin zarafin mutane izuwa yanzu, babban ci gaba a yaki da cin zarafin mata da Yara kana’na shine hada hannu tare don magance matsalar.
Duk wanda ke da hannu a cin zarafin mata da Yara kanana, wanda ya aikata laifin da wanda aka chiwa zarafin, da sauran iyalai duk suna karkashin kulawar gwamnati ne, kuma babu wanda ke da hakkin ya hana a yi shari’a a kansa kamar yadda duk wani yunƙuri ya tanadar na a kai ga kama shi tare da tuhumar shi da yanke masa hukunci a kotu.
Babu wanda ke da hakkin ya ce sun rufe ko sakaye lamarin cin zarafin jinsi a tsakanin mata da ‘yan mata, dole ne a fuskanci tanadin Shari’a dama ci gaba da gabatar da kara har zuwa karshe.
Ana ganin gwamnati a duk matakai, musamman Gwamnatin Jihar Bauchi, tana hada gwiwa da abokan jera tafiya da kungiyoyin kasa da kasa domin kara karfafa wadannan dokoki da tsare-tsare da ake da su na kare mata da ‘yan mata daga duk wani nau’in tashin hankali na cin zarafin su.
A dukkanin sassan Gwamnati akwai bukatar a cigaba da samar da horo da kuma maidahankali ga waɗanda suka fuskanci cin zarafin jinsi walau mata ko maza.
Gwamnati ta himmatu wajen kawo karshen cin zarafin da mata da ‘yan mata, ke fuskanta hakan ya nuna kwarin gwiwar gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, na kafa dokar ta-baci a bangaren Ilimi. Hakan tasa aka sami gagarumar nasara yayin da ake samun tago mashi a sassan ilimi tare da ƙwarewa, kuma an samar da wuraren koyo da koyaswa da suka dace da cigaban Ilimi a idon duniya.
Rashin Ilimi ga al’ummar dake fuskantar koma baya, shine babban dalilin da yasa ‘yan mata da mata suke fuskantar cin zarafi jinsi, amma ko shakka babu lamarin na iya canzawa muddum suka sami Ilimi mai inganci.
Wannan yana nuna niyya da sha’awar kawar dq duhun da ke cinye wadanda ake mulkinsu muddum idan aka tashi tsaye ta wannan fuska.
2_ Kara wayar da kan jama’a da bayar da shawarwari, masu fafutuka, kungiyoyin farar hula, kafafen yada labarai da kungiyoyin addini suna hada kai don wayar da kan jama’a da bayar da shawarwarin kawo karshen cin zarafin mata,Yara kanana da sauran ‘yan mata.
Suma Sarakuna Iyayen kasa. Ba a bar su a baya ba, masarautun gargajiya suna bada kima matuka ga Iyaye mata da kuma ba da himma don kare haƙƙinsu da rayuwar su baki daya.
Wannan shine kalaman Maigirma Dan Jikan Bauchi, Hussaini Abubakar othman, kuma Hakimin kasar Miri, a lokacin da na tambayeshi matsayin masu rike da sarautun gargajiya kan mugunyar matsalar nan ta cin zarafin mata da ‘yan mata a Najeriya.
A cewarsa, masarautun gargajiya sun fi tasiri a kan mutane domin babu wani mutum da ba ya karkashin wata masarauta ko wanene shi kuwa.
Ta fuskar tsari a nan din ma masarautun gargajiya suna da rawar takawa wajen alkinta rayuwar al’ummar su. tare da magance matsalar cin zarafin mata da ‘yan mata da daukar mataki da kuma yin abun da ya kamata a bangaren mahukunta muddum lamarin yafi karfin su, a matsayin masu kashin al’ummar su.
Ya kara da cewar, suna hada karfi da karfe da kungiyoyin gwamnati da ofishin uwargidan Gwamnan Jihar don tabbatar da cewar an gurfanar da duk wadanda ake zargi da aikata laifin fyade, cin zarafi jinsi, tada tarzoma da kawo gibi ga sha’anin zaman lafiya da sauran laifuka, yana cewar ko shakka babu a na samu ci gaba sakamakon goyon baya da shugabanci na kwarai da masu ruke da sarautun gargajiya keyi wa al’ummar su.
Ana girmama masarautun gargajiya sosai saboda suna da amana kuma suna da ikon kiran kowa, salon shugabanci ne na rayuwa wanda babu wata jama’a da za ta yi alfahari da samun koma baya a cikin ta, kuma masarautun gargajiya sune idon al’umma.
Daga bi sani Basaraken sai ya bukaci mata da ‘yan mata har’ma da magidanta mata da maza da su dauki ladabi da kunya, dasaka tufafi masu rufe jiki da kyau sukuma sa ido sosai kan ‘ya’yansu don kubutar da su daga hare-haren masu cin zarafin jinsi
a matsayin tasu gudunmuwar wajen yaki da duk wani nau’in tashin hankali musamman na mugunyar lamarin nan na cin zarafin jinsi.
3. Samar da tallafi ga waɗanda suka fuskanci cin zarafin jinsi:
ƙungiyoyi suna taka muhimmiyar rawa wajen magance cin zarafin jinsi, kamar bada shawarwari, kula da lafiya da tallafawa a fagen shari’a ga waɗanda suka fuskanci cin zarafin jinsin baki daya.
Kungiyar mata musulmi ta Najeriya wato (FOMWAN),kungiya ne da ke da niyyar gani cewa duniya ta bada muhimmanchi wajen karfa mata da kananan yara mata da duk wani ilmantarwa dama tallafi don samun dogaro da kai. Ta yi kulafucin cewar al’ummar duniya zasu karfafi mata da yara da matasa. A lokacin da aka karfafi mata da ‘yan mata da sana’oin hannu ko shakka babu ta hakane za’a kawo karshen aikace-aikacen ta’addanci da cin zarafin jinsi a matakin farko.
Daya daga cikin babban manufar kungiyar ta FOMWAN shi ne baiwa mace musulma damar zama muryar marasssa murya wajen alkinta rayuwar su, la’akari da haka kungiyar ta mayar da hankali wajen samar da tallafin karatu, da shirya tarurruka don tantance al’amuran daka iya kawo cikas musamman wadanda suke da alaƙa da cin zarafin mata da ‘yan mata.
Hajiya Habiba Usman Sa’ad, itace Shugabar kungiyar ta FOMWAN reshen Jihar Bauchi, ta lissafo sassa da dama da kungiyar ta samar da suka hada da kwamitin sulhu, kwamitin tsara shirye-shirye da suka shafi samari da za su iya zama jakadu na kwarai don magance aikata laifin cin zarafin jinsi da kuma kare ‘ya’ya mata ga kowane nau’i na fadawa cikin haɗarin rayuwa.
A cewarta, yawancin mambobin kungiyar FOMWAN sun rungumi wadanda suka tsira daga cin zarafin jinsi musamman mata da Yara kanana ta hanyar magance ƙalubalen rashin wurin da za a ajiye su don gyara rayuwar su.
Wani fanni na ci gaba shi ne tsarin hada kai da duk wadanda suka tsira ta hanyoyin mika kai ta hanyar hadin gwiwa da wani shashin mata na kungiyar kiristoci ta Najeriya, WOWICAN, don kula da wadanda suka tsira daga kiristoci da kuma yin cudanya da masu shari’a da ma’aikatan kiwon lafiya don samar da kulawar data dace, tallafin kiwon lafiya da zamantakewa ga wadanda abin ya shafa da kuma gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban kuliya manta sabo.
Alkaluma sun nuna raguwar cin zarafin mata da ‘yara kana’na kamar yadda Cibiyar tantancewa da kula da wadanda aka ci musu zarafi ta jihar Bauchi ta sami rahoton cin zarafin jinsi wato (SGBV) daya kai dari 200 daga watan Fabrairu zuwa Nuwamba na shekara ta 2023 sabanin wasu alkaluma masu ban tsoro da aka samu a shekarun da suka gabata kuma ta lura cewa ana yawan samun wadannan kararraki a yankuna masu nisa saboda talauci da rashin samun ilimi.
Gidauniyar ci gaban mata da matasa ta IKRA ta bayar da rahoton cewar, kungiyar ta samu rahoton cin zarafin jinsi wato SGBV sama da dari 500 a shekarar 2023, inda akalla 100 daga cikin wadan da aka ciwa zarafin mata ne da suke kananan hukumomin jihar (an buga rahoton a ranar 15-10-2023).
Duk da wannan ci gaba, akwai sauran jan aiki da za a yi a kan cin zarafin mata da Yara kana’na Kuma matsala ce mai sarkakiya wacce ke bukatar nazari.
Ƴan jarida, na himmatuwa wajen ci gaba da haskaka wannan mugunyar al’amari,kuma a matsayina na yar jarida ina kira ga masu fada aji a wannan tafiyar, da masu fafutuka, da daidaikun jama’a da su zo mu hada hannu tare wajen yin yaki da duk wani nau’in cin zarafin jinsi a tsakanin mata da yara kanana a Jihar Bauchi da ma kasar Najeriya.
Melody Agwom Dauda melodyagwom5@gmail.com 08139978610.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.