Home Labarai Kungiyar likitoci masu neman kwarewa sun janye yajin aiki da suka shiga

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa sun janye yajin aiki da suka shiga

 

Shugabancin kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya NARD ta dakatar da yajin aikin gargadi na mako guda da ta fara a ranar Laraba 17 ga watan Mayu.

Shugaban kungiyar, Dokta Emeka Orji, ya shaida wa gidan talabijin na Channels ta wayar tarho cewa kungiyar ta dakatar da matakin na tsawon makonni biyu ne kawai bayan sun cimma matsaya da gwamnati a ranar Juma’a.

Sai dai ya bayyana cewa likitocin za su sake haduwa a rana ta biyu ga watan Yunin wannan shekarar domin duba cigaban da aka samu tare da yarjejeniyar da aka sanya wa hannu, kafin daga bisani kungiyar ta yanke matsaya na gaba.

Likitocin dai na bukatar a biya su dukkanin wani alawus na albashin su, tare da inganta kayayyakin more rayuwa cikin gaggawa a asibitocin gwamnati.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.