Abdul Tech Systems Ltd
Labarai World News

Kur’anai Sama Da 30,000 Aka Raba Ga Masu Ibadah A Saudi Arabia

Published by Abdullahi Yahaya

Hits: 0

Sarkin Saudiyya da ke kula da masallatai guda biyu mafi daraja a duniya, wato masallacin Ka’aba da ke Makka, da na Manzon Allah SAW da ke birnin Madina, ya bada kyautar littafin Al-Qur’ani mai girma sama da 30,000.

An bada qur’a nan ne a matsayin kyauta ga wadanda suka kai ziyara masallatan biyu daga farkon watan Radaman, ga zuwa yanzu kamr yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Kwafin Al-Qur’ani mai tsarki da madba’ar sarki Fahad ta wallafa a birnin Madina, kyuata ce ta musaman daga jagoran kula da masallatan wato sarki Salman bin Abdul’aziz al-Sa’ud ga bakin da suka shigo kasar.

About the author

Abdullahi Yahaya

Seasoned Blogger. Software Developer. Web Designer & Developer. Cybersecurity Expert. Database Engineer. IT Enthusiast.

Leave a Comment