Kwamandan Boko Haram da ya yi sanadin kashe mayaƙan kungiyar 82 a rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a tsakaninsu ya miƙa wuya ga sojoji.
Amir din Tsibirin Bukkwaram ya miƙa wuya ga sojojin Najeriya da ke Rundunar Haɗin Gwiwar Ƙasashe (MNJTF) ne tare da iyalansa da wasu mayaƙa, inda suka sallama makamansu da dabbobi.
“Don kashin kanya ya mika wuya tare da iyalansa da wasu mayaka kuma sun sallama makamansu da dabbobi,” in ji wata majiyar soji, wadda ta ce suna hannun dakarun rundunar Operation Haɗin Kai na MNJRF da ke Monguno, Jihar Borno.
Ta ci gaba da cewa, “Cafke Amir ɗin Bukkwaram gagarumar nasara ce saboda yana cikin manyan miyagun kwamandojin Boko Haram masu fikira kuma yana cikin masu ɗaukar mayaƙa a yankin Tafkin Chadi.”
Aminiya ta kawo rahoton yadda rikicin ƙabilanci na cikin gida a ƙungiyar Boko ya sa mayakanta 82 kashe juna a Jihar Borno.
Rikicin ya ɓarke ne bayan Amir Bukkwaram ya sa an harbe wasu mayaƙansa bakwai ’yan ƙabilar Buduma bayan yunƙurinsu na miƙa wuya ga sojoji bai yi nasara ba.
Matakin ya haddasa ƙazamin faɗan ƙabilanci tsakanin mayaƙa ’yan kabilun Buduma, Fulani, Kanuri da Hausawa a inda 82 daga cikinsu suka mutu.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.