State News

Mu Hada Kai Mu Kwace Kujerar Gwamna a Bauchi : Sarkin Arewa

Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Bauchi, Hassan Mohammed Sheriff, ya roki masu ruwa da tsakin jam’iyyar dasu hada kai gami da aiki tare domin karbe kujerar gwamna a shekara ta 2023 a jihar.

Da yake jawabi, wa manema labaru a sakatariyar yan jarida dake Bauchi, game da rikicin shugabanci daya dabaibaye jam’iyyar, Hassan Sheriff yace samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023 zai taimaka wa jiharnan dore bisa gwadaben daya dace.

Yace, a daidai lokacin da Najeriya ke shirye-shiryen babban zaben shekara ta 2023, ya kamata membobin jam’iyyar suyi karatun ta nitsu da masu raba kawunansu wadanda basu da ruwa cikin jam’iyyar.

Jigon a jam’iyyar ta APC, wanda ya kalubalaci sabbin shugabannin jam’iyyar a kotu, bisa zargin cewa, wasu da basu bada wata gudumowa ba wajen gina jam’iyyar, yanzu suna kawo rudani cikin jam’iyyar a Bauchi.

Hassan Sheriff, ya roki shugaba Buhari daya tsoma baki cikin dambarwar jam’iyyar a jihar, ya kuma nuna goyon baya ga kudirin majalisar kasa na yin amfani da tsarin kato-bayan-kato wajen zaben fidda gwani na jam’iyya.

Leave a Reply