Home Labarai Mutum 5 sun Mutu bayan da Masallaci ya rufta kan Masallata a...

Mutum 5 sun Mutu bayan da Masallaci ya rufta kan Masallata a Zaria

Daga Mu’azu Abubakar Albarkawa, Kaduna

 

Aƙalla mutane 5 ne zuwa yanzu aka tabbatar da mutuwar su, bayan da saman masallacin Juma’a na Kofar Fadar Sarkin Zazzau ya rufta wa masallata lokacin da suke Sallar La’asar a ranar juma’ar nan.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce ginin ya fado ne lokacin da jama’a ke Sallar La’asar a cikin masallacin.

Ya ce tun a ranar Alhamis da ta gabata, aka sanar da shi labarin ganin alamar tsagewar gini a cikin masallacin,kuma da jin hakan, ya umarci ɗaya daga cikin masu rike da sautun gargajiya a Masarautar Zazzau Arc Haruna Idris, Barde Kerarriyar Zazzau ya je don duba inda aka samu matsalar.

Sai dai a cewar Sarkin,ba inda ya tsage ne ma ya rushe ba, wani wuri ne na daban.

A cewar Sarkin,gini ne da ya ɗauki sama da shekaru 100 da gina shi, kuma lokaci daban-daban musamman lokacin damina ginin na yoyo

A cewar shi lokacin da lamarin ya faru, sun dawo kenan daga buɗe wani masallacin Juma’a a garin Turawa da ke gundumar Soba, ya shiga gida kenan ba jimawa ake sanar da shi labarin.

“an samu gudunmawar Jama’a da jami’an tsaro da kuma dukkanin hukumomin da ya kamata lokacin da lamarin ya faru”, a cewar Sarkin Zazzau.

Da yake ƙarin haske kan lamarin, Abdulmumin Adamu Sakataren shiyyar Zariya na kungiyar bada agajin gaggawa ta red cross, ya ce, mutane da dama ne suka jikkata lokacin da lamarin ya faru, wato lokacin da ake raka’a na biyu ne na Sallar La’asar.

Sai dai ya ce, akwai wanda basu sami rauni sosai ba kuma tuni ma suka cigaba da harkokinsu, yayin da wasu ke asibiti suna samun kulawa da likitoci.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.