Kungiyar tsaro ta NATO ta sanar da abin da ta kira babban garambawul ga tsarin rundunar tsaronta ta hadin guiwa, tun bayan yakin cacar baka.
Sakatare-Janar na kungiyar, Jens Stoltenberg ya bayyana Rasha a matsayin mafi muhimmanci da kuma barazana ta kai tsaye ga tsaro da martabar ƙungiyar.
Ya ce NATO za ta kara yawan dakarunta zuwa dubu dari uku a matsayin shirin ko ta-kwana – tare da inganta rundunonin yaƙinta da kuma tanadin makamai a mambobin ƙungiyar na gabashi.
Za a amince da sabbin dubarun na Nato ne a taron Madrid da za a yi wannan makon, wanda kuma zai diba barazanar China ga Nato.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.