Labarai

NNPCL ya ciyo bashin dala biliyan uku daga bankin AFREXIM

Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da bankin Afreximbank mai hada-hadar kayayyaki a ciki da wajen Afrika don samar da dala biliyan uku ta gaggawa da za a biya bashin ɗanyen mai da su.

Wata sanarwa da NNPCL ya fitar a yau Laraba ta ce an ƙulla yarjejeniyar ne a hedikwatar bankin da ke birnin Alƙahira na ƙasar Masar.

Kamfanin ya ce wannan yarjejeniya za ta taimaka wa shirin gwamnatin Najeriya na samar da daidaito a kasuwar canjin kuɗi da kuma bunƙasa darajar naira.

A makon da ya gabata darajar nairar ta yi faɗuwa mafi muni a tarihi, inda aka canzar da dala ɗaya kan N970 a kasuwar bayan fage – kafin ta ɗan farfaɗo zuwa N790 a ranar Talata.

Lamarin na faruwa ne tun bayan da Shugaba Tinubu ya sauya tsarin canjin kuɗin zuwa na kasuwa ta yi halinta kan darajar naira a watan Yuni.

BBC Hausa

Leave a Reply