Home News NOA Ta Yaba wa EFCC Kan Yaki da Laifukan Intanet

NOA Ta Yaba wa EFCC Kan Yaki da Laifukan Intanet

Daga Ude Ogbonnaya Israel

Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) ta yaba wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) bisa nasarar da ta samu a kwanan nan wajen rusa wani gungun masu aikata laifukan intanet da ke aiki a ƙasar nan.

NOA ta bayyana cewa wannan nasara ta nuna gagarumar alama cewa Najeriya ba za ta lamunci kowanne irin laifi ba, ba tare da la’akari da kasar da masu aikata laifin suka fito ba.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa da Hulɗa da Jama’a na hukumar NOA, Bala Musa, ya fitar, hukumar ta bayyana cewa Najeriya a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta da tsayuwa akan doka, tana da nauyin kare mutuncinta da martabarta a idon duniya.

Musa ya bayyana cewa ko da yake NOA na ci gaba da wayar da kai kan ɗabi’a ta gari da kuma alhakin zama ɗan ƙasa nagari ta hanyar nuna muhimmancin riko da martabar a ci gaba da gangamin wayar da kan jama’a da take yi, yana da matuƙar muhimmanci ga ’yan Najeriya da ma baƙi su girmama dokokin ƙasar tare da guje wa duk wani aiki da zai iya cutar da tsaron kasa ko kuma tauye darajar al’uma.

“Masu aikata laifukan intanet, ko su ’yan ƙasa ne ko kuma baƙi, dole su gane cewa hukumomin tsaro na cikin shiri, na da kayan aiki, kuma suna da ƙuduri wajen kamo duk wanda ya aikata laifi. Najeriya ba za ta zama mafaka ko wurin gudanar da mugayen ayyuka ba,” in ji sanarwar.

Ya ƙara da kiran shugabanni, sarakunan gargajiya, cibiyoyin ilimi, ƙungiyoyin fararen hula da kuma kafafen yada labarai da su ci gaba da yaɗa bayane kan riko da darajar Najeriya, kishin ƙasa da ɗaukar nauyin ci gaban ƙasa.

Musa ya kara da cewa; “muna yabawa EFCC bida wannan jajircewa da suka nuna. Ta haka ne kasashe ke ginuwa – ta hanyar daukar tsauraran matakai wajen tabbatar da bin doka da oda”.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.