’Yan kasuwa a Buckingham, yankin Fadar Masarautar Ingila, sun ce rasuwar Sarauniya Elizabeth II, ya kawo musu karin ciniki.
Masu shaguna da otel-otel a Buckingham da ke birnin London sun ce cikinsu ya karu sosai tun bayan rasuwar sarauniyar har zuwa lokacin da aka kaddama da babban danta, a matsayin sabon sarki —Charles III.
Sun ce karin cinikin ya shafi bangaren abinci zuwa masu neman masauki da masu sayen furanni da saurnan kayan kyaututtuka da ke dauke da hoton marigayiyar.
Manajar kamfanin Cool Britannia, masu kayan kyaututtukan alfarma da ke Buckingham, Patricia Hajali, ta shaida wa kafar yada labarai ta DW cewa ana rububin sayen “Duk abin da ke dauke da hoton Sarauniya,” musamman rigunan T-Shirt da kananan kofuna da zobuna da maballai da sauransu
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.