National News

Shugaba Buhari Zai Tafi Landan

Published by Abdullahi Yahaya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Landan da ke kasar Birtaniya domin ganin likitocinsa na tsawon mako biyu.

Mai tallafawa Shugaban a fanni watsa labarai, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce shugaban zai wuce birnin Landan ne bayan halartar wani taro a kasar Kenya.

Ya ce Shugaban Buhari zai bar Abuja ranar Talata domin halartar taron Shirin Majalisar Dinkin Duniya a Kan Muhalli (UNEP) karo na 50, wanda za a yi tsakanin uku zuwa hudu ga watan Maris din 2022 a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Femi ya ce Buhari zai halarci taron ne biyo bayan gayyatar da Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya yi mishi.

A cewar sa, Shugaba Buhari, yayin tafiyar, zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama, da Minista Ma’aikatar Muhalli, Sharon Ikeazor, da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya, Ambasada, Ahmed Rufa’i Abubakar, da kuma Shugabar Hukumar da ke Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa.

Yayin taron na kasar Kenya dai, ana sa ran Buhari zai gabatar da jawabi kan matsayin Najeriya a bangaren kare muhalli, kamar yadda ya zo daidai da taken taron na bana.

Ana sa ran taron zai duba kalubalen muhalli a duniya cikin shekaru 50 din da suka gabata bayan kafa hukumar.

About the author

Abdullahi Yahaya

Seasoned Blogger. Software Developer. Web Designer & Developer. Cybersecurity Expert. Database Engineer. IT Enthusiast.

Leave a Comment