Tattalin arzikin Najeriya na tafiyar hawainiya sakamakon hauhawan farashin kayayyaki da ke tasiri wajen ma’aunin tattalin arzikin GDP da kashi 3.54 cikin 100 a zago na biyu na wannan shekarar, idan aka kwatanta da kashi 5.01 cikin 100 a 2021.
A cewar rahoton hukumar kididdiga ta kasa, NBS a Najeriya hauhawan farashi da annobar korona sun yi tasiri wajen sake durkushewar tattalin arzikin Najeriya.
A watan Yuli ma sai da hukumar ta fitar da irin wannan rahoton da ke nuna yadda hauhawan farashi ya karu a Najeriya da kashi 19.64 cikin 100
Hukumar ta ce idan aka kwatanta hauhawan farashin da na bara, an samu karin kashi biyu da doriya cikin dari, kasancewar na bara ya kai fiye da kashi 17 cikin dari.
Hauhawan farashin, kamar yadda rahoton ya nuna ya fi shafar kayan abinci, irin su biredi da dankali da doya da sauran dangogi mabunkasa kasa da nama da kifi da man gyada da sauransu.
Kayan abin ce da na amfani, wadanda ya fi tashi, kamar yadda alkaluman suka nuna sun hada da iskar gas da man disel da kudin mota da na jirgin sama da tufafi da kuma kudin wanki da guga.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.