Labarai

Tinubu ya naɗa Badaru ministan tsaro

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa tsohon Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru ministan tsaron ƙasar.

Kazalika, tsohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ne zai taimaka masa a matsayin ƙaramin ministan tsaro.

Tsohon Gwamnan jihar Ribas da ke kudancin ƙasar, Nyesom Wike, shi ne ministan Abuja, yayin da Maryam Mairiga daga Kano za ta yi aiki a matsayin ƙaramar ministar Abuja.

Wata sanarwa ce daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana sunayen ministocin da ma’aikatunsu a yammacin Laraba.

Mutum 45 majalisar dattawa ta tantance kuma ta tabbatar a matsayin ministocin na Tinubu, abin da ke nufin za a sanar da sauran nan gaba.

Ga jerin sunayen ministcoin da ma’aikatunsu:

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin na Dijita – Bosun Tijani

Ƙaramin Ministan Muhalli – Ishak Salaco

Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki – Wale Edun

Ministar Harkokin Teku da Tattalin Arziki – Bunmi Tunji

Ministan Lantarki – Adedayo Adelabu

Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma – Tunji Alausa

Ministan Ma’adanai – Dele Alake

Ministan Yawon Buɗe-Ido – Lola Ade-John

Ministan Sufuri – Adegboyega Oyetola

Ministan Kasuwanci da Zuba Jari – Doris Anite

 

Leave a Reply