Sports

Za’a Horas Da Alkalan Wasa 600 Gabanin Kakar Wasan Bana

Kungiyar alkalan wasa ta Najeriya, ta fara gwajin motsa jiki ga sama da alkalan wasa 600 gabanin kakar wasanni da suka fito daga jihohin arewa, da ke gudana a nan Bauchi.

Horon wanda ke kimtsa alkalan wasan a zahiri da koshin lafiya, shine sharadi na farko domin zaben alkalin wasa kafin hura kowacce gasa.

Da yake magana wa manema labaru a filin wasa na tunawa da Sir. Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi Mr. Tari Azeez yace, an zabi Bauchi ne domin gudanar da gwajin saboda kayakin wasa da suke jibge kuma ake bukata.

Da yake tsokaci, shugaban sashin alkalan wasa hukumar wasanni ta kasa, Zubairu Sani, yace wannan shine karon farko da yankin arewa maso gabas ya karbi bakuncin taron, yace manufar haka shine, sabunta ilimin alkalan wasa, musamman game da canje-canjen da aka samu na dokokin wasanni.

Wasu cikin mahalartan da aka zanta dasu, sun yaba wa kokarin inda suka ce hakan zai dafa musu wajen inganta aikace-aikacen su.

Leave a Reply