Home Sports Erik Ten Hag Ba Zai Fara Da Cin Premier League Ba

Erik Ten Hag Ba Zai Fara Da Cin Premier League Ba

Erik ten Hag ba zai fara harin lashe Premier League a kakar farko a matakin kociyan Manchester United ba, zai dai nemi samun gurbin Champions League.

Ten Hag ya zama kociyan United, wadda ta bayyana nada shi cikin watan Afirilu, domin maye gurbin Ralf Rangnick.

Bayan da ya ja ragamar Ajax ta lashe babban kofin tamaula a Netherlands hudu a shekara biyar – ya soke yarjejeniyar da ta rage masa a Amsterdam domin ya koma United kan lokaci.

Kocin mai shekara 52 da mataimakinsa Mitchell van der Gaag da Steve McClaren, sun kalli wasan karshe a gasar Premier League da United ta yi rashin nasara 1-0 a gidan Crystal Palace.

”Na fada cewar aikin da zan gudanar shi ne yadda zan mayar da United kan turbar da ta taka a baya,” kamar yadda kocin ya sanar.

”Manchester United ta cancanci buga Champions League a koda yaushe, shi ne abin da za mu fara tunkara.”

Da farkon fara kakar bana, United ta nuna cewar za a yi gogayya da ita a lashe Premier League na bana daga baya batun ya canja ta koma rashin kokari.

Rashin kokarin United ya fito karara a kakar nan, tun bayan da Atletico Madrid ta fitar da ita a gasar Champions League a cikin watan Maris.

Tun bayan da United ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gida a hannun Atletico ranar 15 ga watan Maris, wasa biyu kacal ta ci a Premier League aka doke ta karawa biyar.

Cikin wasannin da ta sha kashi har da 4-0 da Liverpool ta caskara ta da wanda itama Brighton ta dura 4-0 a ragar United.

Da haka ne kungiyar ta karkare a mataki na shida a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila, za ta kara a Europa League a badi kenan.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.