Home Labarai Ƴan fashi 13 sun shiga komar ƴan sanda a Zariya

Ƴan fashi 13 sun shiga komar ƴan sanda a Zariya

 

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar cafke matasa 13 bisa zargin hannunsu a harkallar ayyukan kungiyar asiri da fashi da makami a garin Zariya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne ya sanar da hakan a cikin wata takarda da wakilinmu ya samu a Zariya.

Sanarwar ta ce rundunar ’yan sanda da ke Sabon Garin Zariya ce ta cafke wadanda ake zargin.

“Wadanda aka cafke din sun tabbatar da kasancewa ’yan kungiyar asiri ta (Aiye Confraternity) wadanda suke gudanar da mummunan ayyukan su a manyan makarantu daban-daban.

Bayanai sun ce ababen zargin sun zabi unguwar Graceland a matsayin cibiyar gudanar da ayyukan su.

Sanarwar ta kara da cewa, “da misalin karfe 3 na daren ranar 10 ga watan Satumba ne ’yan kungiyar dauke da manyan makamai suka afka unguwar Graceland inda suka rika shiga gidaje suna kwace masu kayayyaki yayin da kuma suka raunata wasu.

“Sun kwace wayoyin hannu, da katin cire kudi na ATM da gwala-gwalai da kudade kafin daga bisani suka tsere cikin daji.”

A cewar sanarwar, “daga nan ne jami’an rundunar ’yan sandan ta bi sahun ababen zargin, inda suka samu nasarar cafke mutum 13 daga cikinsu.”

Jami’in hulda da jama’ar ya ce yanzu haka wadanda aka kama din suna bai wa ’yan sanda hadin kai wajen kokarin kamo sauran ababen zargin da suka arce.

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kaduna, CP Musa Yusuf Garba ya roki iyaye da suka rika sa ido tare da kulawa da irin abokan da ’ya’yansu ke mu’amulla da su don kaucewa shiga ayyukan ta’addanci.

Kwamishinan ’yan sandan wanda ya yaba wa jami’an rundunar bisa gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Kazalika, ya kuma roki al’umma da su rika kokarin sanar da jami’an bisa duk wani al’amari da ba su gamsu da shi ba.

Jaridar Aminiya


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.