Latest:
Labarai

Ƴan bindiga sun kashe mutum bakwai a wani masallaci a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum bakwai yayin da suka buɗe wuta ana tsaka da sallar Isha’i a wani masallaci da ke yankin ƙaramar hukumar Ikara na jihar Kaduna ranar Juma’a.

Wani mazaunin garin da abin ya faru a kan idonsa, ya kuma buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa tuni aka yi jana’izar mutanen kamar yadda addinin musulunci ya tanadar

Ya ce ”Muna cikin raka’ata ta uku a sallar isha’i ne sai ga wasu mutum uku sun shigi cikin masallacin ta ɓangaren arewa, sai kawai suka buɗe wuta inda suka kashe mutum hudu a cikin masallacin”.

“Sai sai mutum guda a waje, sannan kuma suka kashe wani mai mota da ya zo wucewa ta kusa da masallacin, sai wani shi ma da ya taho ta wurin”, in ji ganau ɗin.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar wa BBC faruwar lamarin, tana mai cewa ‘yan bindigar sun kashe ƙarin mutum biyu a cikin garin na Saya-Saya.

Maharan sun shiga garin tun da misalin ƙarfe 5:00 na yamma kafin su kai harin ana sallar Isha’i, a cewar mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ta Kaduna.

“Sai da suka shiga gari suna tambaye-tambaye da tattara bayanai, amma babu wanda ya lura da aniyarsu kafin su kai harin da misalin ƙarfe 8:00 na yamma,” in ji shi.

Rundunar ta yi kira ga mazauna jihar da su dinga saka ido da kuma kai rahoton yunƙurin duk wani abu da ba su saba gani ba.

BBC Hausa

Leave a Reply