Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum bakwai yayin da suka buÉe wuta ana tsaka da sallar Isha’i a wani masallaci da ke yankin Æaramar hukumar Ikara na jihar Kaduna ranar Juma’a.
Wani mazaunin garin da abin ya faru a kan idonsa, ya kuma buÆaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa tuni aka yi jana’izar mutanen kamar yadda addinin musulunci ya tanadar
Ya ce ”Muna cikin raka’ata ta uku a sallar isha’i ne sai ga wasu mutum uku sun shigi cikin masallacin ta Éangaren arewa, sai kawai suka buÉe wuta inda suka kashe mutum hudu a cikin masallacin”.
“Sai sai mutum guda a waje, sannan kuma suka kashe wani mai mota da ya zo wucewa ta kusa da masallacin, sai wani shi ma da ya taho ta wurin”, in ji ganau Éin.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar wa BBC faruwar lamarin, tana mai cewa ‘yan bindigar sun kashe Æarin mutum biyu a cikin garin na Saya-Saya.
Maharan sun shiga garin tun da misalin Æarfe 5:00 na yamma kafin su kai harin ana sallar Isha’i, a cewar mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ta Kaduna.
“Sai da suka shiga gari suna tambaye-tambaye da tattara bayanai, amma babu wanda ya lura da aniyarsu kafin su kai harin da misalin Æarfe 8:00 na yamma,” in ji shi.
Rundunar ta yi kira ga mazauna jihar da su dinga saka ido da kuma kai rahoton yunÆurin duk wani abu da ba su saba gani ba.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








