Labarai

Ƴan Boko Haram sama Dari Biyar sun Mika Wuya Wa Sojin Najeriya

 

Kimanin Yan ta’addar Boko Haram dari biyar da goma sha daya da iyalansu ne suka mika wuya bayan wani farmaki da sojojin Najeriya suka kai a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Adadin wadan da suka mika wuyar ya kunshi manya maza 99, manyan mata 161, da yara 251 a wurare daban-daban.

An bayyana hakan ne a ranar Alhamis ta cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Musa Danmadami ya fitar.

Ya ce a daya daga cikin hare-haren, sojojin sun kashe ƴan ta’addar Boko Haram guda 26 da ‘yan ta’adda , sun kama wasu ’yan ta’adda 25 da ke ba da kayan aikin sa kai da kuma dan leken asiri guda daya.

A cewarsa, duk kayayyakin da aka kwato, wadanda aka kama, da kuma ‘yar makarantar Chibok da aka ceto an mika su ga hukumar da ta dace domin ci gaba da daukar mataki yayin da ‘yan ta’addan Boko Haram da suka mika wuya aka bayyana ‘yan uwansu tare da mika su ga hukumar da ta dace.

Leave a Reply