Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Masu Sanya Ido Dubu Bakwai kan shirin NSIP

 

Gwamnatin tarayya ta dauki masu sa ido guda 7500 masu zaman kansu don kula da shirye-shiryenta na zuba hannun jari, wato NSIPs a turance a fadin jihohi 36 dake fadin kasa.

Ministar harkokin jin kai, da ci gaban jama’a Hajiya Sadiya Umar-Farouq ce ta bayyana hakan a birnin Abuja a farkon wani taron bita na masu sanya idano masu zaman kansu.

Sadiya Faruk tace don tabbatar da samun nasara tare da inganta tasirin shirye-shiryen zuba jari na kasa, ma’aikatar ta samar da ingantaccen tsarin sanya ido da tantancewa a matakai uku na gwamnati.

Tawagar shugaban shirin kuma mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa akan sa ido da tantancewa, Fatiya Askederin da kodineta na shirin zuba jari na kasa Dr. Umar Bindir sun yabawa masu sa ido bisa jajircewarsu ga shirin.

Leave a Reply