Latest:
Labarai

Ƴan sanda sun kama wadanda ake zargi da sace daliban Jami’ar Jos

Ƴan sandan sun kama wadanda ake zargi da sace daliban Jami’ar Jos

An kama wasu ƴan bindiga da ake zargin su da hannu a sace ɗaliban Jami’ar Jos da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Ƴan bindigan biyu na cikin mutum 91 da aka kama kan aikata mugwayen laifuka daban-daban a yankin, a yayin da dakarun tsaro ke zafafa kai samame kan wasu ƙungiyoyin masu tayar da zaune tsaye.

An kama waɗanda ake zargi da sace mutanen ne bayan wani samame da aiki na musamman da aka ƙaddamar na tsawon wata guda, da suka yi sanadin da jami’an tsaro suka gano maɓoyarsu, kamar yadda mai magana da yawun wata rundunar soji ta musamman a Jihar Filato da ake kira Operation Safe Haven ya faɗa a wata sanarwa.

Satar mutane don neman kuɗin fansa

Sace-sacen mutane don karɓar kuɗaɗen fansa inda har ɗaliban jami’a ma ba su tsira ba, ya zama ruwan dare a Nijeriya.

An saki waɗanda aka sace daga Jami’ar Jos ɗin bayan da iyayensu suka bai wa ɓarayin wasu kuɗaɗe da ba a faɗi yawansu ba, kamar yadda kafafan yaɗa labaran ƙasar suka ce.

Satar mutane don karɓar kuɗin fansa da ƴan bindiga ke yi har yanzu wani babban ƙalubale ne ga jami’an tsaro a Nijeriya, inda a wasu lokutan har a kan kashe mutanen da aka sace ɗin.

Ƴan sandan Nijeriya na ba da shawarar cewa bayar da kuɗin fansa da ake yi ga masu satar mutanen kan rura wutar matsalar, inda suke gaya wa iyalan waɗanda aka sace cewa su daina biyan kudin fansar.

TRT Afrika