Home Labarai Ƴan sanda sun kama wadanda ake zargi da sace daliban Jami’ar Jos

Ƴan sanda sun kama wadanda ake zargi da sace daliban Jami’ar Jos

Ƴan sandan sun kama wadanda ake zargi da sace daliban Jami’ar Jos

An kama wasu Æ´an bindiga da ake zargin su da hannu a sace É—aliban Jami’ar Jos da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Ƴan bindigan biyu na cikin mutum 91 da aka kama kan aikata mugwayen laifuka daban-daban a yankin, a yayin da dakarun tsaro ke zafafa kai samame kan wasu ƙungiyoyin masu tayar da zaune tsaye.

An kama waÉ—anda ake zargi da sace mutanen ne bayan wani samame da aiki na musamman da aka Æ™addamar na tsawon wata guda, da suka yi sanadin da jami’an tsaro suka gano maÉ“oyarsu, kamar yadda mai magana da yawun wata rundunar soji ta musamman a Jihar Filato da ake kira Operation Safe Haven ya faÉ—a a wata sanarwa.

Satar mutane don neman kuÉ—in fansa

Sace-sacen mutane don karÉ“ar kuÉ—aÉ—en fansa inda har É—aliban jami’a ma ba su tsira ba, ya zama ruwan dare a Nijeriya.

An saki waÉ—anda aka sace daga Jami’ar Jos É—in bayan da iyayensu suka bai wa É“arayin wasu kuÉ—aÉ—e da ba a faÉ—i yawansu ba, kamar yadda kafafan yaÉ—a labaran Æ™asar suka ce.

Satar mutane don karÉ“ar kuÉ—in fansa da Æ´an bindiga ke yi har yanzu wani babban Æ™alubale ne ga jami’an tsaro a Nijeriya, inda a wasu lokutan har a kan kashe mutanen da aka sace É—in.

Ƴan sandan Nijeriya na ba da shawarar cewa bayar da kuɗin fansa da ake yi ga masu satar mutanen kan rura wutar matsalar, inda suke gaya wa iyalan waɗanda aka sace cewa su daina biyan kudin fansar.

TRT Afrika


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.