Wasu ƴanbindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe mutane 21 a Baton da Rayogot da ke gundumar Heipang a karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Plateau.
Rwang Tengwong, sakataren yada labarai na kungiyar Berom Youth Movement, BYM, wata kungiyar cigaban al’adu da zamantakewa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a yau Alhamis a Jos.
Tengwong ya ce harin da aka kai kan al’umomin ya faru ne da karfe 1:26 na safiyar yau Alhamis, kuma ya yi sanadin jikkata wasu mutane bakwai.
Tengwong, wanda ya yi tir da hare-haren ba gaira ba dalili a wasu sassan jihar, ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar.
“Mutane 21 ne aka kashe a wani hari da aka kai a wasu kauyuka biyu a gundumar Heipang da ke Barkin Ladi.
“Maharan, wadanda suka zo da misalin karfe 1:26 na safe sun kashe mutane 17 a Batin na garin Heipang yayin da aka kashe wasu hudu a Rayogot.
A martanin da ya mayar kan lamarin, Gwamna Caleb Mutfwang na Plateau ya yi Allah-wadai da hare-haren tare da yin kira ga jami’an tsaro da su zakulo wadanda suka kai harin tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Daily Nigerian Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.