Home Siyasa 2023: Dan Takarar Jam’iyyar NNPP Zai Kayar Da Zulum A Jahar Borno...

2023: Dan Takarar Jam’iyyar NNPP Zai Kayar Da Zulum A Jahar Borno — Kwankwaso

Ya bayyana haka ne a Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno, jim kadan bayan ya kaddamar da hedkwatar jam’iyyar ta jihar ranar Asabar.

A ranar Alhamis ce dai Hukumar Raya Birane ta Jihar Borno ta kulle hedkwatar, amma daga bisani ta sake bude ta bisa umarnin Gwamna Zulum.

A cewar Kwankwaso, “Ina mai tabbatar muku cewa da yardar Allah, in kuka zabi dan takarar Gwamnanmu da Sanatocinmu guda uku da ’yan majalisar tarayyarmu guda 10 da na majalisar jiha guda 28 da kuma dan takararmu na Shugaban Kasa, zan mayar da jihar Borno kamar Kano.

“Wannan ziyarar ta nuna wa duniya cewa Allah Ya kawo mana canjin da muke bukata. Irin dandazon mutanen da muka gani tun daga mashigar Maiduguri har zuwa tsakiyar gari ya nuna yadda mutanen Borno ke mararin canji.

“Na ga yadda matasa, yara da ma sauran al’ummar Borno suka rika yin tattaki tun daga filin jirgi, wasu ma a kafa suka je filin don tarbarmu.

“Babban abin da yake zuciyata a yanzu shi ne ta yaya wadannan matasa da yaran za su koma makaranta? Ta yaya za mu dawo da wutar lantarki ta dindindin a jihar Borno? Ta yaya za mu dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas da ma Najeriya baki daya.

“Wadanda suke kawo wa jihar Bono koma-baya har yanzu suna nan sun fito suna so su ci gaba da abin da suka saba amfanar da ’yan tsirarun mutane. Abin da muke son yi shi ne mu gyara wannan tsarin ta yadda kowanne dan jihar zai amfana,” inji Sanata Kwankwaso.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.