Siyasa

Zaben Najeriya: Atiku Abubakar Ya Yi Bulaguro Zuwa Birnin Landan

Sa’o’i kadan bayan da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi wata ganawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a birnin Landan na kasar Birtaniya, an rawaito cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya nufi Landan din shima.

Wata jaridar yanar gizo, The Cable, ta ruwaito cewa wata majiya daga wani makusancin Atiku ta bayyana cewa Atikun na da kudirin ganawa da gwamnan na Ribas.

PDP Ta Shiga Fargaba Bayan Wike Ya Yi Ganawar Sirri Da Tinubu
2023: A Shirye Muke Mu Bude Kofar Kulla Kawance Da Sauran Jam’iyyu Kafin Zabe –NNPP
“Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya tafi Landan bayan ya baro birnin Paris. Ana sa ran zai gana da Wike a wani yunƙurinsa na warware matsalolin da ke tsakaninsu,” in ji majiyar.

Sai dai hadiman Atiku kan harkokin yada labarai ya musanta batun ko yana da niyyar ganawa da Wike domin sasantawa da shi kan rikicin da ya taso daga zaben da dan takarar shugaban kasa ya yi na gwamnan jihar Delta, Sen Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimakinsa.

Leave a Reply