Latest:
Siyasa

Shugaban Kwamitin Amintattu Na Jam’iyyar PDP Ya Yi Murabus

Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibril ya yi murabus daga mukaminsa.

Sanata Walid Jibril ya sauka daga kujerar tasa ce ranar Alhamis, a daidai lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin da take kokarin dinkewa.

Yabayyana cewa ya yi murabus ne domin kauce wa kazancewar matsalar da kuma tabbadar da ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar ya lashe zaben 2023.

Jam’iyyar PDP da Atiku na tsaka mai wuya, a kokarinsu na dinke barakar da biyo bayan zaben Atiku a zaben dan takarar shugaban kasar jam’iyyar.

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda shi ma  ya yi zawarcin kujerar ya bayyana bacin ransa kan yadda Atiku ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takarsa.

A yayin da Atiku da jam’iyyar ke kokarshin shawo kansa, Wike dai ya ki bayar da kai bori ya hau.

Bai tsaya nan ba, ya yi kira da Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Iyiorchia Ayu ya yi murabus daga mukaminsa, wanda shi kuma ya ce ba za ta sabu ba.

A gefe guda kuma ana zargin Wike da yunkurin goyon bayan ’yan takarar shugaban kasan jam’iyyun APC mai mulki, Bola Tinubu da kuma dan takara Jam’iyyar Leba, Peter Obi.

Leave a Reply