Jagoran jamâiyyar APC na kasa kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jamâiyyar, Bola Tinubu, ya taya tsohon Mataimakin Shugaban Kasa murnar lashe zaben fid da gwanin jamâiyyar PDP, inda ya ce yana nan yana jiran shi su fafata.
Ya bayyana haka ne a sakonsa na taya murna ga Atikun, jim kadan bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar Asabar.
Atiku dai ya samu nasarar samun tikitin takarar Shugaban Kasa na jamâiyyar PDP ne da aka gudanar a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.
Tinubu dai ya yaba wa Atiku saboda kishin kasarsa da kuma yadda ya jajirce wajen ganin Najeriya ta kai ga tudun-mun-tsira, tare da yaba wa ragowar âyan takarar kan yadda zaben ya gudana lami lafiya.
Sai dai Tinubu ya ce yana sa ran fafatawa da Atikun a babban zabe mai zuwa matukar daliget din APC suka zabe shi a zaben da za a yi a makon nan.
Ya ce nasarar Atikun ba ta zo masa da ba-zata ba, laâakari da gogewarsa da kuma gwagwarmayar shi a fagen takarar Shugaban Kasa tun a shekarar 1993.
Ya ce, âYayin da muke tunkarar babban zabe mai zuwa, ina kira ga dan takarar PDP da ma ragowar âyan takara da a yi siyasa ba da gaba ba.
âSai dai PDP ta yi rashin saâa, ita da dan takararta ba sai sun bata wa kansu lokacin bayanin me zai sa a zabe su ba, bayan sun lalata shekara 16 babu wani abin a-zo-a-gani.
ââYan Najeriya na sane da irin badakalar da PDP ta tafka a shekara 16, kuma wannan zai yi matukar kawo wa kamfen dinsu tarnaki.
âAmma duk da haka, ina taya tsohon Mataimakin Shugaban Kasarmu murnar lashe zaben a jamâiyyarsu,â inji Tinubu.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.


