Siyasa

Bukola Saraki Ya Taya Atiku Murnar Lashe Zaben Fidda Gwani A Jam’iyyar Su

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma daya daga cikin wadanda suka nemi takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Bukola Saraki, ya taya dan takarar jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar murnar lashe zaben fid da gwanin jam’iyyar.

A ranar Asabar ce dai Atiku ya lashe ya zama dan takarar PDP a zaben 2023 mai zuwa bayan ya kayar da su Sarakin da sauran ’yan takara, yayin zaben da aka gudanar a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.

Atiku ya lashe zaben dan takarar shugaban kasar PDPAtiku: Karo 6 a shekara 30 na neman kujerar shugaban kasa 2023: Ina nan ina jiranka mu fafata  sakon Tinubu ga Atiku.

Saraki ya kuma gode wa dukkan abokansa da magoya bayansa a fadin kasar nan kan yadda suka ba da himma wajen samar da manufarsa ta kawo sauyi da ake kira: #RealSolutions da #FixNigeria!

Ya kara da cewa, “Yayin da muke shirin tunkarar babban zaben gaba, ina alfahari da cewa sakonmu na #RealSolutions da jagoranci na gari ya ratsa zukatan miliyoyin matasan Najeriya a fadin kasar nan.

“Yanzu, dole ne mu hada kan dukkan ’yan takararmu a fadin kasar nan don gyara tattalin arzikinmu, mu dakile matsalar rashin tsaro da kuma kawo karshen tsadar rayuwa,” inji shi.

Bukola Saraki ne dai ya zo na uku a zaben da kuri’a 70 a zaben fid da gwani na Shugaban Kasa na jam’iyyar, wanda ’yan takara 14 suka fafata a cikinsa.

Leave a Reply