Siyasa

2023: Ina Jiranka Mu Fafata — Tinubu Ga Atiku

Jagoran jam’iyyar APC na kasa kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar, Bola Tinubu, ya taya tsohon Mataimakin Shugaban Kasa murnar lashe zaben fid da gwanin jam’iyyar PDP, inda ya ce yana nan yana jiran shi su fafata.

Ya bayyana haka ne a sakonsa na taya murna ga Atikun, jim kadan bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar Asabar.

Atiku dai ya samu nasarar samun tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP ne da aka gudanar a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.

Tinubu dai ya yaba wa Atiku saboda kishin kasarsa da kuma yadda ya jajirce wajen ganin Najeriya ta kai ga tudun-mun-tsira, tare da yaba wa ragowar ’yan takarar kan yadda zaben ya gudana lami lafiya.

Sai dai Tinubu ya ce yana sa ran fafatawa da Atikun a babban zabe mai zuwa matukar daliget din APC suka zabe shi a zaben da za a yi a makon nan.

Ya ce nasarar Atikun ba ta zo masa da ba-zata ba, la’akari da gogewarsa da kuma gwagwarmayar shi a fagen takarar Shugaban Kasa tun a shekarar 1993.

Ya ce, “Yayin da muke tunkarar babban zabe mai zuwa, ina kira ga dan takarar PDP da ma ragowar ’yan takara da a yi siyasa ba da gaba ba.

“Sai dai PDP ta yi rashin sa’a, ita da dan takararta ba sai sun bata wa kansu lokacin bayanin me zai sa a zabe su ba, bayan sun lalata shekara 16 babu wani abin a-zo-a-gani.

“’Yan Najeriya na sane da irin badakalar da PDP ta tafka a shekara 16, kuma wannan zai yi matukar kawo wa kamfen dinsu tarnaki.

“Amma duk da haka, ina taya tsohon Mataimakin Shugaban Kasarmu murnar lashe zaben a jam’iyyarsu,” inji Tinubu.

Leave a Reply