Home Labarai Mazauna Kalaba sun shiga zullumi kan satar Mazaƙuta

Mazauna Kalaba sun shiga zullumi kan satar Mazaƙuta

 

Mazauna Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba sun shiga zullumi sakamakon annobar satar mazakuta da ake zargin ta kunno kai a birnin.

Lamarin dai ya jefa jama’a, musamman maza manya da yara cikin dimuwa da shakkar waye zai zo kusa da kuma wacce irin mu’amala ce za ta sa a kusanci juna.

Tun makon da ya gabata aka rika baza jita-jitar satar, sai ga shi kwatsam a unguwar Hausawa da ke birnin, sun sace na wani mai suna Abbas Shitu da na kanensa Sani Shitu.

Wasu mutane ne dai ake zargin sun je shagonsu sayayya, amma bayan sun kammala ciniki sun tafi ke nan, sai jikin su Abbas da Sani ya ba su wani iri, su na shafa gabansu suka ji ba su ji mazakuntarsu ba.

Nan take suka ankarar da jama’ar da ke wajen aka yi katarin cafke wadanda ake zargi aka kai su gaban sarkin Hausawa da ke unguwar shi kuma ya kirawo ’yan sanda aka tafi caji ofis dinsu da ke yankin.

Aminiya tayi ƙoƙarin jin ta bakin mahaifiyar yaran saboda hankali ba kwance yake ba, ta ce ba za ta iya cewa komai ba.

Wata majiya ta ce mutanen da ke gudanar da wannan mummunar sana’a suna sayar da mazakutar kan Naira 600.

Kazalika, lamarin ya sanya kasuwar namijin goro ta bude inda yawanci ’yan asalin jihar kan saye shi su saka a aljihu suna yawo da shi ko kuma kanumfari a matsayin dafa’i daga barayin.

Sai dai Cosmos Ekpang, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar da kuma Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta bakin Kakakinta, Irene Ugbo, sun karyata faruwar hakan inda suka ce wannan duk soki-burutsu ne.

Likitoci kuwa a nasu bangaren, su ma sun ce ba su yarda hakan na iya faruwa ba.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, akwai rashin yadda da juna tsakanin jinsin maza musamman a Kalaba bayan bullar annobar.

Jaridar Aminiya


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.