Rundunar Æ´an sanda a jihar Katsina ta bukaci alâumma da su yi watsi da wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta na zargin karkatar da kayan tallafin abinci da jamiâanta ke yi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jamiâin hulda da jamaâa na rundunar, PPRO, ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya fitar.
Rundunar Æ´an sandan ta ce faifan bidiyon ba kawai yaudara ba ne, an fitar da shi ne da nufin bata sunan Æ´ansanda.
âBayan cikakken bincike, an gano cewa buhunan shinkafar da aka gani a bidiyon a cikin motar âyan sanda an kama su ne daga hannun wasu Éatagari.
âWasu marasa gaskiya sun yi samu fiye da kason su na kayan agajin , shine Æ´an sanda suka kama suka kuma mayar da su wurin da aka raba.
âSaboda haka abinda bidiyon ta nuna ba shi bane gaskiyar lamari kuma yunÆuri ne na kushe kyakkyawan ÆoÆarin jamiâan da aka tura wurin don ba da tallafi, Éaukar matakan tsaro da tabbatar da gudanar da taron lafiya,â in ji âyan sanda.
Rundunar Æ´an sandan ta kuma tabbatar wa jamaâa cewa zarge-zargen da aka yi a cikin wannan faifan bidiyo Æarya ne.
Daily Nigerian Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









