Gwamnatin Tarayya ta ce akwai yiwuwar ta ciyo bashin Naira tiriliyan 11.3 domin cike gibin kudaden shigar da za ta samu a kasafin kudin 2023.
Hakan na nufin gibin ya zarce na kasafin 2022 na Naira tiriliyan 7.35 da fiye da kaso 100.
MinistarKudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ce ta sanar da haka, lokacin da take gabatar da daftarin matsakaicin tsarin kashe kudade (MTEF&FSP) na shekarun 2023 zuwa 2025, a gaban Kwamitin Kudi na Majalisar Wakilai ranar Litinin.
Zainab ta kuma ce la’akari da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, ana hasashen cewa gibin kasafin zai kai kusan Naira tiriliyan 12.41, a maimakon tiriliyan 7.35 na kasafin 2022.
Ta kara da cewa, “Jimillar kudaden da ake sa rai Gwamnatin Tarayya za ta kashe a 2023 su ne tiriliyan 19.76.
“A cikin haka kuma, ana hasashen gibin kasafin ya kai tiriliyan 11.30 a 2023, kari a kan tiriliyan 7.35 na kasafin 2022.
“Hakan na nufin kaso 5.01 na ma’aunin tattalin arziki na GDP, wanda kuma ya haura kaso uku cikin 100 da aka tanada a Dokar Kashe Kudade (FRA), ta 2007,” inji Zainab.
Dangane da batun tallafin mai kuwa, Ministar ta ce akwai yiwuwar gwamnatin ta kashe Naira tiriliyan 3.36 ko kuma tiriliyan 6.7 a 2023.
Sai dai ta koka cewa kudaden da Najeriya ke samu daga cinikin danyen mai na raguwa duk kuwa da farashinsa na karuwa a kasuwar duniya.
Ta alakanta hakan da kalubalen da ake fuskanta wajen hako man da kuma yawan kudaden da NNPC ke kashewa wajen biyan tallafi.
Kazalika, Ministar Kudin ta koka cewa duk da Najeriya na kashe Naira biliyan 3.2 wajen gadin bututan mai, kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.
Da yake nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar, James Abiodun Faleke, ya ce la’akari da halin da Najeriya ke ciki, ya zama wajibi ta lalubo dukkan hanyoyin fadada kudaden shigar ta.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.