Labarai

Ambaliyar ruwa ya hana samada mutane 500 kwana a gidajensu a Cheledi

Ambaliyar ruwa tayi sanadiyar hana mutane sama da 500 kwana a gida jensu a daren jiya a cikin garin Cheledi dake Karamar Hukumar Kirfi a Jihar Bauchi.

Hakan ya biyo bayan shafe wassu awanni ana maka ruwan sama Kamar da bakin kwarya.

Wannan abu dai ba sabon abu bane a wurin Al’ummar garin na Cheledi domin kuwa an dauki sama da Shekaru biyar ana fama da wannan matsalar ta Ambaliyar Ruwa.

Lokuta da dama dai Al’ummar garin sun nemi agaji daga Gwamnati, amma har ya zuwa yanzu babu wani abunda ya sauya.

Leave a Reply