Labarai

Kidayar 2023: Za Mu Kashe Kimanin N21bn Don Shata Taswirar Najeriya – Farfesa Yemi Osinbajo

Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira biliyan 21 domin shata taswirar yadda kidayar jama’a ta 2023 za ta gudana.

Osinbajo ya kuma ce duk da haka, akwai bukatar karin kayan aiki da karin hanyoyin samun kudi kwarara ga hukumar da ke kula da aikin.

Osinbanjo ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja, a taron da Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta shirya, mai taken Goyon Bayan Tsarin Kidayar Jama’a a Najeriya”.

Mataimakin Shugaban Kasar na musmaman a harkokin yada labarai, Laolu Akande, wanda shi ne ya wakilici Osinbajon ya ce gwamnati ta sahale a cire Naira biliyan 198 daga kasafin kudin bana, kuma tuni ta saki kaso 60 cikin 100 na kudin.

Ya kuma ce, “Daga nan zuwa 2050, ana sa ran yawan ‘yan Najeriya zai kai miliyan 400, don haka dole ne gwamnati ta ci gaba da bayar da ingantaccen ilimi, da harkar lafiya da kuma abinci.

“Haka kuma akwai bukatar inganta bangaren tsaro, da samar da aikin yi ga matasa, wadanda su ne ke da fiye da rabin kason Najeriya.

“Don haka kidayar na da muhimmacnci sosai  a wannan gaba, kuma shiri na musamman da  tattara bayanan da suka kamata abu ne mai muhimmanci sosai, wajen samar da ci gaba mai dorewa da cigaban kasa.

A nasa bangaren, shugaban hukumar ta NPC, Nasir Kwarra, ya ce taron ya tattauna batutuwan da suka shafi tafiyar da kidayar a abadi, da kuma shirye-shiryen tunkarar kalubalen da aikin ke tattare da shi.

Leave a Reply