Latest:
Labarai

An daka wawa kan motocin shinkafar tallafi a Kwara

 

Wasu bata-gari sun daka wawa a kan wasu motoci uku da ke dauke da shinkafar da za a raba tallafi a wasu yankunan Jihar Kwara.

Bayanai sun nuna lamarin ya faru ne a yankunan Oja-Oba/Idi-Ape/Isale-Oja da ke Kananan Hukumomin Ilorin ta Gabas da Ilorin ta Yamma.

Aminiya ta rawaito cewa an kwashe kayan ne wajen misalin ƙarfe 6:30 na yammacin Juma’a, a dab da ofishin ’yan sanda na ‘C’.

Mutanen dai sun yi wa motocin kirar Toyota Dana kwanton bauna ne, lokacin da suke dauke da kananan buhunan shinkafar masu nauyin kilogiram 10, a kokarinsu na wucewa don zuwa wasu yankunan Jihar.

A cikin bidiyon, an ga bata-garin suna jejjefa wa jama’a buhunan, yayin da su ma suka debi kason su ba tare da wani ya taka musu birki ba.

Mazauna yankin sun ce daga bisani ’yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda suka yi tambayoyi, kodayake ba su kama kowa ba.

Aminiya ta ce da wakilinta ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce ba su da masaniya

Leave a Reply