Noah Kekere, likitan nan da ake zargi da yanke kodar wata mara lafiya a Jos, ya koma mahaukaci da rana tsaka lokacin da yake tsare a hedkwatar âyan sandan Jihar Filato.
An kama Noah ne ranar Laraba, bayan wani rahoton korafi da aka kai asibitin Nasarawa Gown bisa zargin cire kodar wata mata yayin wani aikin tiyata a shekara ta 2018.
Tun da farko dai Rundunar âYan Sandan Jihar ta tabbatar da kama wanda ake zargi da yanke kodar ba bisa kaâida ba.
Sai dai lokacin da ake bincike a kan shi a hedkwatar âyan sandan a ranar Asabar, Noah ya fara nuna alamun tabin hankali.
Hakan ce ta sa aka saka masa ankwa sannan aka garzaya da shi sashen kula da masu matsalar kwakwalwa na Asibitin Koyarwa na Jamiâar Jos (JUTH) domin a duba lafiyarsa.
Wata majiya daga hedkwatar âyan sandan ta ce an garzaya da wanda ake zargin asibiti ne lokacin da ya fara nuna alamun hauka, yana yayyaga kayan jikinsa a ofishin âyan sanda.
Wata majiya daga asibitin ita ma ta tabbatar da cewa tuni suka karbi mutumin kuma yanzu haka yana can ana kula da shi.
Wakilin jaridar Aminiya ya rawaito cewa tuni âyan sandan kwantar da tarzoma suka yi wa sashen da aka kwantar da likitan a asibitin kawanya.
Da aka tuntubi Kakaki Rundunar âYan Sandan Jihar, DSP Alabo Alfred, bai amsa tambayar wakilinmu ba a kan lamarin.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








