HaÉaÉÉiyar Daular Larabawa ta cire haramcin biza a kan ‘yan Najeriya, kamar fadar shugaban Najeriya ta bayyana.
Wata sanarwa daga fadar shugaban ta United Arab Emirates (UAE) ta Éauki matakin ne bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da takwaransa Mohamed bin Zayed Al Nahyan a yau Litinin a birnin Abu Dhabi.
“Kazalika, wannan yarjejeniyar na nufin kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na Etihad da Emirates za su ci gaba da shiga da fita a Najeriya nan take,” in ji sanarwar da Ajuri Ngelale ya fitar.
Ta Æara da cewa yarjejeniyar ba ta Æunshi biyan wani kuÉi ba a nan kusa tsakanin Æasashen, yana mai nuni da miliyoyin dalolin da gwamnatin Najeriya ta riÆe wa kamfanonin jiragen na kuÉin tikiti.
Kusan shekara Éaya ke nan da UAE ta dakatar da bai wa matafiya daga Najeriya biza, a rikicin da ya samo asali tun daga lokacin annobar korona.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








